ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ministan man fetur na kasar AUE Suhail al-Mazrouei ya na cewa bukatar danyen man fetur a duniya bi sa hasashen kungiyar a shekara ta 2021 ba zai tafi kamar yadda aka tsara ba, saboda kara yaduwar cutar korona a kasashen duniya.
Suhail al-Mazrouei ya kara da cewa, wannan halin da muke ciki da alamun zai kai har rubu’i na farko ko fiye da haka na shekara mai zuwa ta 2021. Don haka kungiyar ta na tunanin za ta rage yawan man da ake haka.
342/